Kungiyar kare hakkin bil adama ta Syrian Observatory tace jiragen yaki sun kai samame sau 60 a cikin kasa da sa’o’i uku a yankuna kudancin kasar mai tarin jama’a.
Shugaban kugiyar Observatory, Rami Abdel Rahman yace ana amfani da gine ginen 'yan tawayen da mayakan jihadin yayin wannan hari. Rahman yace wadannan hare haren sune mafi muni tun bayan wani mummunar harin da aka kai a ranar goma ga watan Agusta da ya kashe akalla fararen hula 53 ciki har da kananan yara a Idlib da kuma wani lardi a Aleppo dake kusa da wurin.
Galibin yankunan Idlib da kewaye yana hannun yan tawayen ne da suka hada da kungiyar Hayat Tahrir al-Sham da kuma kawancen kungiyoyin 'yan bindiga a Syria, wanda a can baya take da alaka da al-Qaida.
Itama Rasha ta fada a jiya Asabar cewa, tana da sahihin bayani cewa, 'yan tawayen na Syria suna shirin kai wani harin takala a Idlib, domin tabbatar da taimako da sukje samu daga kasashen yammacin duniya
Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Rasha Igor Konashenkov, yace duk wadanda suke da hannu a cikin harin takalar, su dada shiri kan shiri daga yammacin jiya Asabar takwas ga watan Satumba.
Facebook Forum