Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Halin Da Ake Ciki A Yammacin Gabar Kogin Jordan Na Kara Tabarbarewa - MDD


Volker Turk
Volker Turk

A jiya Talata babban jami'in kare hakkin 'bil adama na MDD yayi gargadin halin tauyen hakkin da ake fuskanta a gabar yamman kogin Jordan ciki harda yankin gabashin birnin Kudus na kara tabarbarewa yayin da ake cigaba da fuskantar mace-mace da wahalhalun babu gaira babu dalili a zirin Gaza

Babban kwamishinan kiyaye hakkin bil adama na majalisar dinkin duniyar, Volker Turk, ya shaidawa taron bude tattaunawar kwamitin kare hakkin dan adam na majalisar cewar, "halin da ake ciki a gabar yamma ta kogin Jordan ciki harda gabashin birnin kudus, yana kara tabarbarewa."

A cewarsa, izuwa 15 ga watan Yunin da muke ciki, jami'an tsaron Isra'ila sun hallaka falasdinawa 528, 133 daga cikinsu yara kanana tun cikin watan Oktoban daya gabata, abinda a wasu lokutan ke kara sabbaba tsananin damuwar kisan gilla.

Ya kara da cewar an hallaka Yahudawa 23 a hare-haren Falasdinawa a gabar yamma ta kogin Jordan ko cikin Isra'ila.

Turk yace yayi matukar mamaki game da rashin mutunta dokokin kasa da kasa dana jin kai daga bangarorin dake rikici da juna a gaza.

Turk ya cigaba da cewar, hare-haren Isra'ila babu kakkautawa a gaza sun haddasa dimbin wahalhalu da barna kuma ta cigaba da hanawa da kange shigar da kayan agaji zuwa yankin."

Ya kara da cewar, kungiyoyin Falasdinawa masu fafutuka da makamai na cigaba da yin garkuwa da mutane, ciki harda a wurare masu cunkoson jama'a, abinda ke kara jefa rayuwar wadanda aka yi garkuwa dasu da fararen hula cikin hatsari.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG