Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hare-Hare da Jiragen Saman Yaki ya Hallaka Mutane a Kalla 24


Garin Kobani a Siriya, 26 ga Oktoba, 2014.
Garin Kobani a Siriya, 26 ga Oktoba, 2014.

Kungiyar lura da abubuwan da suka shafi hakkokin bil Adama a kasar Syria...

Kungiyar lura da abubuwan da suka shafi hakkokin bil Adama a kasar Syria ta ce wasu hare-haren da jiragen saman yakin gwamnatin kasar suka kai lardin Homs da yammacin jiya Asabar sun hallaka mutane 24 a kalla.

Kungiyar ta fada a yau Lahadi cewa mutane 16 da suka kunshi yara 10 da mata 6 sun mutu a garin Talbisa sanadiyar luguden wutar da jiragem saman yakin gwamnatin kasar Syria suka yi. Kuma kungiyar ta ce daga cikin mutane 24 da suka mutu, 16 'yan gida daya ne.

A garin Wa'er ma hare-haren jiragen saman yakin sun kashe mutane 6. Daga cikin su 3 'yan gida daya ne.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG