Hukumomin Najeriya sun karyata jita-jitar da ake yada cewa, Najeriya ta hana kasashe kamar Cadi shigowa Najeriya domin ta yaki 'yan bindiga.
Darektan cibiyar bayanai ta Najeriya, Mike Omeri ne ya karyata jita jitar, a hira da yayi da wakilin Sashen Hausa Umar Farouk Musa. Yace Najeriya yanzu haka, tana gudanar da shawarwari da kasashe makwabta, da nufin tsara hanyoyin tunkarar matsalolin da 'yan binidgar suke haddasawa ga kasashen duka.
Mike Omeri yace babu abunda ya gagari sojojin Najeriya, matsalar itace ta rashin kayan yaki. Al'amarin d a yace shugaba Goodluck Jonatahan sani sosai, uma ana kokarin ganin an wadata sojoj da kayan aiki. Omeri, yace ai saboda karin kayan aiki ne yasa aka fara samun nasarori a wasu sassa inda ake fafatawa da 'yan binidgar.
Mike Omeri yace, jama'a su gane matsalar ta'addanci bata tsaya a Najeriya kadai ba, ya bada misali da kasashe kamar Iraqi da Syria, inda 'yan kungiyar ISIL ko ISIS suke ta kama kasa.