Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malaman Makarantun Firamaren Abuja Sun Gudanar Da Zanga-Zanga Akan Bashin Kudaden Albashi


Malaman da su ke gudanar da zanga zanga a dandalin Unity Fountain da ke Abuja
Malaman da su ke gudanar da zanga zanga a dandalin Unity Fountain da ke Abuja

A talatar nan ne, malaman firamare a babban birnin tarayyar Najeriya, suka gudanar da zanga-zanga a dandalin “Unity Fountain” dake Abuja.

A yayin zanga-zangar, malaman sun zargi Kananan Hukumomin Abuja da yin wasarere da batun jin dadi da walwalarsu.

Malaman sun gudanar da zanga-zangar ne akan rashin biyansu bashin da suke bi na kudaden albashi dana karin girma da kuma na mafi karancin albashi tun daga shekarar 2019.

Malaman sun bukaci Ministan Abuja, Nyesom wike da Shugaban Kasa Bola Tinubu su sa baki a lamarin.

Haka kuma sun yi kira da a sake fasalta tsarin ilmin firamare a kasar, inda suka bukaci gwamnatin tarayya ta kwace ragamar gudanar da makarantun daga hannun kananan hukumomi.

Malaman firamaren birnin Abuja sun shafe fiye da mako guda suna yajin aiki amma har yanzu sun ce babu wani takamaiman martani daga hukumomin da alamarin ya shafa.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG