An jiyo masu zanga-zangar da suka hada da mata da matasa suna rera wakokin gwagwarmaya, a yayin da jami’an tsaro ciki harda ‘yan sanda ke kallo.
A cewar masu zanga-zangar, hauhawar farashin kayan masarufi da rashin daukar kwakkwaran mataki daga bangaren gwamnati ya sanyasu datse manyan hanyoyi da nufin janyo hankalin gwamnatin ta sauraresu.
A jawabinsa ga masu zanga-zangar, Mataimakin Gwamnan Jihar Neja, Yakubu Garba, yace gwamnati tana sane da irin mawuyacin halin da al’umma ke ciki a halin yanzu.
Ya kara da cewar gwamnati na aiki tukura wajen ganin ta sassauta matsalar tsadar rayuwa da mawuyacin halin da janye tallafin man fetur ya haifar.
Dandalin Mu Tattauna