MINNA, NIGERIA - Wata sanarwa daga Kakakin ‘Yan Sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ta nuna sun kama wata Aisha Jibrin mai shekaru 30 da suka ce ita ce ta tsara yadda aka gudanar da wannan zanga-zangar.
Sauran matan sun hada da Fatima Aliyu yar shekaru 57, da kuma Fatima Isyaku mai shekaru 43. Ko baya ga wannan dai ‘yan sandan sun ce sun kama wasu matasa 24 da suke zargin suna da hannu wajan shiga wannan zanga-zanga.
Dama dai tini gwamnatin jihar Nejan ta ce masu zanga-zangar ta ranar Litanin sun yi ne domin satar kayan wata babbar mota kamar yadda gwamnan jihar, Umar Bago ya bayyana mana.
To sai dai masu sharhin akan lamura sun yi Allah wadai da kama wadannan mata.
Kabiru Abubakar wani mai sharhi kan lamuran jihar Neja da daya daga cikinsu.
Itama dai kungiyar kare hakkin ‘dan adam a jihar Neja ta bayyana rashin jin dadinta akan kama wadannan mutane kamar yadda Shugaban Kungiyar na jihar Neja Kwamred Abubakar Abdullahi ya shaida mana.
Rudunar ‘yan sandan dai ta ce da zarar ta kammala bincike akan mutanen zata gurfanar da su ne gaban kotu domin fuskantar hukunci.
Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:
Dandalin Mu Tattauna