Yace muhawararsu ta jiya ta kasance ne kan yadda za'a tafiyar da zaman nasu da kuma ka'idojin zaman da kuma yadda zasu dinga amsar kudure-kudure. Yayi misali da abun da shugaban kasa ya fada masu inda yace kafin wata yarjejeniya ta sami karbuwa to sai kashi uku cikin hudu na wakilan sun amince. Idan aka samu kashi uku cikin hudu wato kashi 75 cikin 100 lokacin ne kudurin zai zama tabbatacce da za'a iya yin aiki da shi.
Saidai a cikin wakilan akwai wadanda basu yadda da furucin shugaban kasa ba domin akwai wadanda suke ganin idan an hakikance kan samun kashi 75 cikin 100 kafin a karbi kuduri to hakan zai yi wuya taron kuma zai kasance bashi da wani anfani domin an kawo wani abun da zai hana duk wani kuduri karbuwa. Sun kawo nasu shawarar sai dai bata karbu ba. An tsaya kan wannan abun da shugaban kasa ya fada.
Alhaji Ghali yace har yanzu ba'a gama ba domin littafi ne guda suke aiki a kai. Da aka tambayeshi ko yana gani zasu gama muhawararsu su kaiga jawabin shugaban kasa sai yace matsalar ita ce shugaban taron da mataimakinsa babu wanda ya san yadda ake gudanar da irin wannan taron wanda ya yi kama da na majalisun dokoki. Saboda rashin kwarewarsu ana kwan gaba kwan baya a taron. Yace amma akwai irinsa da suke da kwarewa kan aikin majalisa a cikin taron sabili da haka a hankali a hankali zasu cigaba.
Wata ukun da aka basu kamar ya yi kadan har a ce za'a iya tattauna duk matsalolin Najeriya kana a samu a lalubo bakin zaren warwaresu. Amma yace duk da haka ba za'a ce baya yiwuwa tunda za'a kafa kwamitoci.
Ga karin bayani