Da alamu kalamun na shugaban kasa basu yiwa wasu gwamnonin dadi ba. Misali, gwamnan jihar Adamawa ta bakin jami'insa mai yada labarai Ahmed Sajoh yace shugaba Jonathan na kokarin rufe kura a gwado ne kawai. Yace kasawar gwamnatin PDP ya jawo tabarbarewar tsaro a kasar. Ya kara da cewa gwamnatin jiha bata da sojoji ko 'yansanda ko SSS ko wasu hukumomi dake da alaka da sha'anin tsaro.Duk manlakar gwamnatin tarayya ne karkashin shugaba Jonathan. Yace abu na biyu sun lura cewa a daidai lokacin da za'a kawo hari a wani wurin sai a janye jami'an tsaro ko kuma a bar 'yan ta'ada su cigaba da kai hari na sa'o'i da dama babu wanda zai tunkaresu koda jami'an tsaro na kusa da wurin.Yayi misali da abun da ya faru a Buni Yadi.
Dangane da zargin cewa ba'a ba matasa ilima ba da ayyukan yi, Ahmed Sajoh yace shugaban kasa yayi rashin gaskiya. Su 'yan kungiyar Boko Haram sun ce basu yadda da ilimin boko ba.Wasu cikinsu sun kone takardun shaidar gama makaranta. Ban da haka kwamitin da shugaban kasa ya kafa na daidaitawa da su karkashin Turaki ai sun sadu da wadanda suka gama jami'a da wadanda ke cikin jami'a amma suka yi watsi da karatun. Kan samarma matasa aikin yi yace gwamnatin tarayya ta fi kowa sakaci.
Shi kuwa gwamnan jihar Borno Kashim Shettima wanda yace baya son yayi jayayya da shugaban kasa yace ai 'yan Najeriya sun san inda matsalar take. Alhaji Isa Gusau mai baiwa gwamnan shawara kan yada labarai yace watakila maganar da aka yada a labarai ba abun da shugaban kasa yace ba ne. Su kuma 'yan ta'adan ai makarantu suke konawa.Idan ko babu makarantu ta yaya za'a ba yara ilimi. Yace maganarsa tana da dauin kai.
Ga karin bayani