Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Uganda ta yiwa madugun adawa Kizza Besigye sabon zargi


'Yansandan Uganda sun cafke madugun 'yan adawa Kizza Besigye
'Yansandan Uganda sun cafke madugun 'yan adawa Kizza Besigye

Babban Lauyan shugaban ‘yan adawar kasar Uganda Dr. Kizza Besigye, yace sabon zargin da akewa wanda yake karewar ya nuna karara cewa wani makirci ne domin a kaskantar da shi game da sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi ran 18 ga Fabrairun bana wanda ake tababarsa.

Kotun Majistare ta Kasangati dake lardin Wakiso ta tuhumi Besigye na jam’iyyar neman canji ta FDC a jiya Labara da cewa ya yiwa umarnin yiwa halartaccen umarnin ‘yan sanda rashin da’a. Kakakin ‘yan sanda Fred Enanga ya fadawa manema labarai cewa an kama Basigye ne a hanyarsa ta zuwa Shelkwatar jam’iyyarsa a makon jiya.

Kakakin yace, muna da shaidar faifan bidiyon da ta nuna Basigye a tsaye a saman motarsa yana yiwa dandazon jama’a bayani ba tare da izinin hukuma ba. Wanda hakan ya sabawa dokar yadda ake aiwatar da taron cikin lumana.

Lauya Peter Mukidi Walubiri dai yace bai gamsu da wannan hujjar ta ‘yan sanda ba, ya ma kara da cewa, ‘yan sandan sun eke ruruta wutar lamarin, ta hanyar tauyewa shugaban ‘yan adawar ‘yancin da kundin tsarin mulkin kasar ya ba shi.

XS
SM
MD
LG