Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansandan Uganda sun jefawa masu kada kuri'u barkonon tsohuwa a zaben da suke yi yau


Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni.
Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni.

‘Yan sanda a babban birnin Uganda sun harbawa masu jefa kuri’a da suka fusata saboda matsalolin da suka fuskanta a rumfunan zabe barkonon tsohuwa.

Rahotanni sun nuna cewa hakan ya faru a wurare da dama a gewayen Kampala a yau Alhamis din nan, yayinda ‘yan Uganda ke kada kuri’a a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalissa.

Wata wakiliyar muryar Amurka Eliizabeth Paulat ta fadi cewa, jami’an tsaro sun harba barkonon tsohuwar bayan da jama’a suka tunkari wajen ‘yan sanda, suna korafin cewa basu sami damar kada kuri’a ba kuma an dauke akwatinan zabe daga rumfuna kafin cikar lokacin da aka bada.

Da farko dai, hukumar zaben Uganda ta fada a wata sanarwa cewa an fara kada kuri’a akan lokaci a yawancin sassan kasar duk da cewa akwai dan jinkirin da aka samu a wasu sassan babban birnin da kuma gundumar Wakiso.

‘Yan kasar uganda fiye da milayn 15 aka yi wa rijista don kada kuri’a a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalissa da kuma na kananan hukumomin da ake yi.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG