Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Takarar Neman Shugabancin Uganda Zasuyi Muhawara


Kizza Besigye Campaign Uganda
Kizza Besigye Campaign Uganda

Kungiyar hada kan addinan kasar Uganda tace muhawarar da aka shirya na shugaban kasa ranar 13 ga wannan watan kafin gudanar da zaben ranar 18 ga wata za a gudanar dashi, duk ko da shugaban kasar Yuweri Museveni baya nan domin kasancewa cikin jerin masu muhawaran.

Shugabannin kungiyar sunce suna nan suna tattaunawa da kungiyar Yan tawaye domin su bari shugaba Museveni ya shiga cikin muhawarar.

Su kace makasudin wannan muhawaran shine domin ya baiwa masu jefa kuriaar damar sanin wani dan takara ne keda manufofin da ya cancanci samun kuriaar su. Tare da kawo karshen kalubalen da ya addabi kasar tasu.

Abinda muhawarar zai mayar da hankali aka sune manufofin kasar game da hulda da kasashen waje, samar da zaman lafiya a duk fadin kasar, tsaro,kasuwanci tsakaninkasar da sauran kasashe, tare da inganta saka hannun jari.

Yanzu haka dai an gayyaci daukacin yan takarar su 8 kafin zaben na shugaban kasa dana ‘yan majilisa.To sai dai abinda wasu ‘yan kasan ke cewa shine ba mamaki shugaba Yoweri Museveni ya halarci muhawarar kamar yadda yaki zuwa na farkon.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG