Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makon gobe za'a gudanar da zaben gama gari na kasar Uganda


Shugaban Uganda Yoweri Musoveni wanda yake neman sake zarcewa bayan ya kwashe fiye da shekaru talatin yana mulki
Shugaban Uganda Yoweri Musoveni wanda yake neman sake zarcewa bayan ya kwashe fiye da shekaru talatin yana mulki

Kasar Uganda na shirin gudanar da zaben gama gari na shugaban kasa da na 'yan majalisu mako mai zuwa

Sauran mako daya ya rage a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa a kasar Uganda, wato ranar 18 ga watan Fabarairun nan, kuma dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta Forum for Democratic Change, Kizza Besigye, wanda ke da magoya baya da yawa a wajen kemfe da gangamin zabe, ya ce yana fargabar ba masu kada kuri’a cin hanci shine babban kalubalen da zai iya samu.

Besigye ya kara da shugaba Museveni a zabuka 3 da aka yi a baya, a shekarar 2001, da 2006, da kuma 2011.

A farkon makon nan, mai magana da yawun gwamnatin Uganda Ofwono Opondo ya ce Jam’iyyar NRM ce zata kara kada jam’iyyar Besigye “bravado” ranar 18 ga watan fabarairun nan.

XS
SM
MD
LG