Rahoton hukumar kidigdiga ya nuna cewa kusan kashi hamsin da shida cikin dari na matasan kasar basu da aikin yi. Wasu kuma kashi tara sun da aiki ne amma kasa da kwarewarsu. Masana kan harkokin zamantakewar al'umma suna danganta tashin tashinan da ake samu da rashin aikin yi na matasa. Dalilin da ya sa ke nan gwamnatin tarayya ta fito da shirin SURE-P.
Shirin zai mayarda hankali ne kan matasa da suka gama makarantar gaba da sakandare domin sake horas da su kan ayyukan hannu da sana'o'i domin su samu abun yi. Jagoran shirin a jihar Gombe Alhaji Adamu Yaro Gombe yace matasa dubu talatin ne zasu ci gajiyar shirin a jihar. Yace wadanda suka gama karatun ko dari nawa ne idan sun yi ragista ta hanyar yanar gizo za'a sama masu abun yi.Yayin da ake horas dasu kowane karshen wata za'a biya kowa nera dubu talatin. Ana bukata su koyi sana'a. Kawo yanzu dai mutane dubu uku suka soma a jihar Gombe.
Wasu iyaye sun yaba da shirin. Alhaji Aliyu Mati yace shirin yana da kyau kuma bisa ga alamu shugabannin shirin a jihar Gombe masu adalci ne. An ga taka rawarsu. Dangane da biyan matasan dubu talatin kowane wata yace da kyau amma horon da za'a basu a basu kan abun da suka karanta.
Wani kuma yace sun gamsu domin sun ga yaran da aka dauka a wancan karon saidai sun bar baya da kura domin an kawo siyasa cikin lamarin. Da sabbin shugabannin kananan hukumomi suka zo sai suka sake tantance yaran suka cire 'ya'yan talakawa suka kawo nasu suka sa abun da ba daidai ba ne. Yace Allah ya ciyar da yara amma kuma sun hanasu. Wancan da ya yi aikin bai sansu ba amma wanda ya zo yanzu yace su ba 'ya'yan kowa ba ne.
Shugabannin SURE-P su uku suna da adalci amma wasu shugabannin kananan hukumomi su ne suke hana ruwa gudu domin sun kawo son kai da nuna ban banci duk da nasu albashin da suke karba suna kyashin dan kalilan da za'a ba yaran.