Alhaji Aliko Dangote ya yi furucin ne yayain da yake zantawa da 'yan jarida a jihar Neja. Ya yi alkawarin yin iyakar kokarinsa domin samarda hanyoyin da tattalin arzikin arewacin Najeriya zai habaka ya kuma cigaba. Yace zuwansa jihar Neja nada nasaba da shirin kafa wata katafariyar gonar shinkafa da za'a yi anfani da ita a kasar baki daya.
Alhaji Dangote yace yanzu sun gane cewa daya daga cikin hanyoyin da za'a fitar da arewa daga talauci ita ce hanyar habaka aikin noma. Sun zo wurin gwamnan jihar Neja su san iyakacin filin da zasu iya samu domin kafa gonar. Nan da 'yan makonni biyu yace gwamnati zata sanarda su. Da alama a kasar Neja za'a iya nomar shinkafa ko sikari.
To saidai bincike da wasu masana suka gudanar ya nuna akwai man fetur kwance a wasu sassa na arewacin Najeriya. Jihar Neja na cikin sassan. Dangane da ko zai shiga harakar hakan man fetur a arewa atajirin yace yana da wannan tunanen to amma kafin lokaci ya kure ya kamata shi ya fara yin wasu abubuwa a arewa kamar yadda yake yi a kudancin kasar. Duk da haka bai fitar da tsammanin shiga harkar mai ba idan lokacin yayi.
Daga bisani Alhaji Dangote yace shirin nan nashi na tallafawa mata masu karamin karfi nan ba da dadewa ba zai iso jihar domin su ma su anfana.