Rayuwa ta gagara a garin domin rashin ruwan sha da abinci da wuraren kwana. Wannan lamarin ya sa mutanen garin sun shiga wani hali na matsanancin rayuwa ganin yadda aka bankawa gidajensu wuta da wuraren kasuwancinsu da ababen hawan jama'a da ma kashe tashar motocin garin da duk motocinsu.
Wakilin Muryar Amurka ya zagaya cikin garin da gwamnan jihar Borno Kashim Shettima da jami'an tsaro da mahukunta. Yayin zagayawar sun gani da idanunsu halin da garin ke ciki. Mutane na zaman jimami da al'ajabi. Wasu kuma sun yi kokarin kafa runfunar zana a kofar gidajensu da aka rusa ko aka kone domin samun wurin fakewa.
Wata anguwa da ake kira low cost wato gidajen da aka gina domin masu karamin karfi cikin gine-gine sittin hudu ne kawai ke tsaye duk sauran an konesu kurmus. Mutanen garin sun ce suna cikin halin kakanikayi banda rashin ruwan sha, man fetur galan daya nera dubu biyu ake sayarwa,. Babu hanyar sadarwa balantana uwa uba wurin kwana.Kwano daya na hatsi nera dari biyu ake sayarwa. Mutanen sun ce sun yi noma amma 'yan Boko Haram sun kone masu hatsi da konakai. Duk abincinsu an kone. Rijiyar burtsatsi dake basu ruwan sha an jefa mata bam. Yanzu mutane basu da wurin kwana ko wurin kasuwanci.
Matan dake cikin garin Bama basu tsira ba. Yawancinsu a rufan suke kwana ko kuma a bakin kofar gidansu. Su ma basu da abinci idan sun je kasuwa su saya ma babu.
Gwamnan jihar ya yiwa mutanen garin jaje. Yace kodayake can baya ya taimaka masu da nera miliyan dari amma yanzu ganin yadda suke zai kara masu nera miliyan dari biyu da alkawarin sake gina garin da duk gidajen da aka kona da wuraren kasuwancinsu.Gwamnan yace baya son kwangila. Kwamitin da ya nada ya yi komi cikin gaggawa da kansu kama abun da ya shafi sayen katako, kwanukan jinka da ma wasu kayan gine ginen domin a sake ginawa mutane matsuguninsu cikin dan lokaci. Ya yiwa 'yan kwamitin kashedi cewa kada su kawo siyasa cikin lamarin.
Wakilin Muryar Amurka yace a kan hanyarsu ta komawa Maiduguri babban birnin jihar Borno sun ratsa wani kauye mai suna Malari cikin karamar hukumar Kondiga inda 'yanbindiga suka kona rabin garin da kasuwarsu daren Asabar da ta gabata. A garin 'yanbindigar sun kashe mutane. A nan ma gwamnan ya jajinta masu da nuna takaicinsa.