Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barazanar Tsagerun Niger Delta Ba Ta Da Amfani - Buhari


Muhammadu Buhari.
Muhammadu Buhari.

Wasu hare-hare da kungiyar ta kai a shekarar 2016, sun gurguntar da adadin man da kasar ke hakowa a rana.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce bai ga dalilin da zai sa kungiyar tsegerun Niger Delta ta yi barazanar kai hare-hare akan bututan man fetur din kasar ba, saboda gwamnatinsa ta riga ta dauki hanyar biya wa yankin bukatun da ya gabatarwa da gwamnati.

Rahotanni da dama sun karade kafafen yada labarai cewa kungiyar tsagerun ta Neja Delta wacce aka fi sani da “Niger Delta Avengers” ta ayyana cewa za ta fara kai hare-hare kan tashoshin man fetur din kasar idan ba a biya mata bukatunta ba.

Wasu hare-hare da kungiyar ta kai a shekarar 2016, sun gurguntar da adadin man da kasar ke hakowa.

“Abin da mamaki a ga cewa barazanar na zuwa ne kasa da sa’a 48 bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da shugabannin yankin na Niger Delta da shugabannin kabilar Ijaw a fadarsa, inda suka tattauna kan muhimman batutuwa.

Karin bayani akan: Niger Delta, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

“Musamman kan kiran da suka yi na a sauya fasalin kasa da kuma kafa wani kwamitin gudanarwa na hukumar raya yankin Niger Delta ta NDDC.” Wata sanarwa da kakakin Buhari Femi Adesina ya fitar a ranar Lahadi ta ce.

A ranar Juma’a 25 ga watan Yuni, Buhari ya gana da shugabannin na Niger Delta da na Ijaw.

“Na kiyaye da bukatu guda goma da kuka mikawa gwamnatin tarayya yayin jawabinku, ina kuma mai ba ku tabbacin cewa, wannan gwamnati ta dukufa wajen samar da maslaharsu.” Shugaba Muhammadu Buhari ya fada a lokacin ganawa da shugabannin, kamar yadda sanarwar ta Adesina ta ce.

Yayin ganawar Buhari har ila yau ya ce, “na kuma damu da yadda aka gurbata nuhallin yankin Niger Delta, kuma kamar yadda kuka sani, an fara aikin share yankin Ogoni, sannan na ba Ministan Muhalli umarnin ya tabbatar cewa an aiwatar da wadannan ayyuka ta hanyar hada kai da al’umomin yankin.”

Rabon da kungiyar ta kai hari kan bututan man kasar tun a shekarar 2017 a cewra Reuters.

XS
SM
MD
LG