Rahotanni daga Najeriya na cewa, Majalisar Wakilan kasar ta janye yin nazari akan kudurin dokar man fetur na PIB da ke gabanta bayan wata ‘yar hatsaniya da ta auku a zauren majalisar.
Bayanai sun yi nuni da cewa ‘yan majalisar dokoki daga kudu maso kudancin kasar, sun nuna adawarsu da rage kason da za a rika ba yankunan da ake hako man fetur a kasar.
An rage ne daga kashi 5 zuwa uku.
Rahotanni sun ce tun gabanin tun gabanin shigowar Kakakkin Majalisar Femo Gbajabiamila, wasu ‘yan majalisar suke ta tafka muhawara kan rage kason, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Lamarin ya kai ga Kakakin ya kira wani taron shugabannin majalisar, wanda daga baya ya yanke shawarar a jingine batun a gefe.
Gabanin daukan wannan mataki, an ji wasu ‘yan majalisar suna daga murya suna waken “kashi biyar, kashi biyar” kamar yadda Channels ya ruwaito.
Sai dai sabanin abin da aka gani a majalisar wakilai, a majalisar dattawa, an amince da rage wannan kaso duk da cewa wasu sanatoci sun nuna adawarsu da sauyin.
Sai dai shugaban majalisar dattawan Sanata Ahmad Lawan, ya ki amincewa da masu adawar, inda ya ce majalisar ta riga ta amince da kudurin.