Shugaban Hadaddiyar Kungiyar 'Yan Kasuwa ta Najeriya, Alhaji Umaru Hussaini Gabari, yace Allah Ya fara kawo musu afuwa, kuma su na addu'ar Allah Ya kawo karshen matsalolin tsaron da kasa take fuskanta a cikin wannan sabuwar shekara.
Sai dai kuma a wani gefen, jama'a a Kano su na kokawa a kan yadda jami'an tsaro, musamman sojoji suke cin zarafin al'umma, wani lokacin ma har da harbinsu ba tare da wata hujja ba.
A ranar larabar nan da ta shige ma, sojoji sun yi harbi kan wasu matasan dake tsaye a gefen hanya su na jiran motar haya, a kan titin Hotoro kusa da NNPC Mega Station, inda harsashi ya huda ma matashi guda gefen cikinsa.
Daya daga cikin matasan da yayi bayanin abinda ya faru ga wakilin Muryar Amurka, Mahmud Ibrahim Kwari, yace sojojin sun zo su na tambayar ko wanene me sayar da kwakwa, amma da suka ce basu bane, su mota suke jira, kawai sai wadannan sojojin suka bude musu wuta.
Amma kakakin rundunar tsaron hadin guiwa ta JTF a Kano, Kyaftin Ikedichi Iweha, yace ba jami'ansu ne suka yi harbin ba, sun ji karar harbi ne kuma da suka doshi can sai suka samu wannan mutumi kwance a kasa an harbe shi, kuma suka kai shi asibiti.
Ga cikakken rahoton nan...