A wata hirar da yayi da MA kakakin ma’aikatar harkokin wajen Ethiopia Dina Mufti ya gayawa Sashen turanci na gidan radiyon nan cewa batun tsagaita wuta da ma wasu batutuwa suna kan ajendar taron.
Wakilan duka sassan biyu a wajen taron, sun bayyana kwarin guiwa kan shawarwarin da za a yi. Jagoran wakilan ‘yan tawaye a taron janar Tabang Deng Gai yace kungiyarsa wacce ta balle daga kungiyar SPLM sun sami sabani da gwamnati. Duk da haka yace ana iya cimma sulhu.
A wani ci gaba, shugaban sudan Omar al-Bashir ya kai ziyara Sudan ta kudu jiya litinin, inda yayi alkwarin kasarsa ba zata goyi bayan ‘yan tawaye daga makwabciyar kasarsa ta kudu ba.
A baya, kasashen biyu sun yi ta sukar juna kan zargin goyon bayan ‘yan tawaye daga daya kasar.
Haka ma a jiya litinin, China tayi kiran da a kawo karshen fada da ake yi a Sudan ta kudu. Kamfanonin kasar Sin sun zuba jari sosai a bangaren makamashi a Sudan ta kudu.