Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lahadin Nan Aka Fara Shawarwarin Sulhu Tsakanin Sassa Biyu Masu Gaba da Juna a Sudan ta Kudu


Wakilan tawagar da take gaba da gwamnatin Sudan ta kudu a Addis Ababa, domin fara shawarwari.
Wakilan tawagar da take gaba da gwamnatin Sudan ta kudu a Addis Ababa, domin fara shawarwari.

Sassa biyu masu gaba da juna a Sudan ta kudu sun fara shawarwarin sulhu a Ethiopia, yayinda ake ci gaba da tarzoma a akalla wurare biyu cikin kasar.

Sassa biyu masu gaba da juna a Sudan ta Kudu sun fara shawarwarin sulhu a Ethiopia, yayinda ake ci gaba da tarzoma a akalla wurare biyu cikin kasar.

A yau lahadi ne sassan biyu zasu zauna teburi guda domin fara shawarwarin sulhun a Addis Ababa bayan jinkirinda aka samu na kwanaki.

Wakilan bangaren shugaba Silva Kiir da na tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar, sun halarci bikin fara shawarwarin da aka yi jiya Asabar.

Mukaddashiyar kakakin Ma'aikatar harkokin wajen Amurka Marie Harf, tace shawarwarin suna da muhimmancin gaske ga jama’ar Sudan ta kudu.

A hira da yayi da Muriyar Amurka kakakin Ma'aikatar harkokin wajen Habsha Dina Mufti, yace manya akan ajendar shawarwarin sun hada da batun tsagaita wuta, da kuma bada dama ga masu aikin agaji su gudanar d ayyukansu, da kuma batun sakin fursinoni.

Jiya Asabar an sami rahotanin cewa ana gwabza kazamin fada kusa da Bor, helkwatar jihar Jonglei dake hanun ‘yan tawaye. Dakarun gwamnatin kasar sun kaddamar farmaki ne da nufin sake kwato garin.

Kamfanin dllancin labaran kasar Faransa yace fashe fashe da karar manyan bindigogin egwa sun girgiza wata gundumar da hukumomin gwamnati suke a Juba babban birnin kasar a jiya Asabar.

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashe dake gabashin Afirka ke take shiga tsakani a shawarwarin.

Wakilin tarayyar turai acan kuriyar Afirka Alexander Rondos yana halartar zaman shawarwarin. Yace hakkin gano bakin zaren a rikicin na Sudan ta kudu yana hanun shugabannin siyasar kasar.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG