A wata wasika da gwamnatin mulkin sojan Nijar ta aika wa Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ne suka sanar masa da matakin bai wa jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya a Nijar Madame Louisse Aubin wa’adin sa'o'i 72, wato kwanaki uku ta tattara kayanta ta bar kasar.
Hukumomin sojan na Nijar sun ce sun dauki wannan matakin ne a matsayin martani ga abin da suka kira zagon kasa da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ke yi bisa tunzurawar kasar Faransa, ta hanyar haramta wa jami’an Nijar shiga zauren taruka na kungiyoyin kasa da kasa na Majalisar Dinkin duniya.
Da yake tsokaci akan wannan batu, Alhaji Sani Gambo masanin harkokin diflomasiyya a Nijar, ya ce Nijar bata da zabi illa daukar irin wadannan matakai.
Ko da yake, Gambo ya kara da cewa matakin zai shafi kasar Nijar sosai duba da yadda ake maida ita saniyar ware tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yuli.
Wannan sabon takun-sakar da aka shiga tsakanin Nijar da Majalisar Dinkin Duniya na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Amurka ta janye tallafin da take ba Nijar na miliyoyin dalar Amurka a fannin tattalin arziki da tsaro da kuma dakatar da horas da sojojin Nijar a fannin yaki da ta’addanci.
A halin da ake ciki, kasashen duniya na ci gaba da maida kasar Nijar saniyar ware, duba da yadda aka hana tawagar Nijar shiga babban taron bankin duniya da asusun bada lamuni na duniya da ke gudana yanzu haka a birnin Marakesh na kasar Morocco.
Saurari rahoton Hamid Mahmoud:
Dandalin Mu Tattauna