Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Neja Ta Rufe Wasu Asibitoci Masu Zaman Kansu


Likitoci da maikatan asibiti suna duban mara lafiya
Likitoci da maikatan asibiti suna duban mara lafiya

Yayin da likitoci ke yajin aikin gama gari a Najeriya sai gashi gwamnatin Neja ta rufe wasu asibitoci masu zaman kansu.

Sama da asibitoci ashirin ne gwamnatin jihar Neja ta rufe saboda saba ma ka'idojin da gwamnati ta tsara masu na yadda zasu gudanar da ayyukansu.

Gwamnatin jihar Neja ta ce ta zakulo wadannan asibitocin ne sanadiyar wani binciken kwa-kwap da ita gwamnatin ta soma yi tun shekarar da ta gabata. Dr. Usman Baba Agaiye, jami'i mai kula da asibitoci masu zaman kansu ya ce tuni ma hukumarsa ta mika masu asibitocin da aka samu da laifi ga 'yansanda domin su fuskanci sharia.

Da yake magana kan laifukan da suka kaiga rufe asibitocin, Dr. Usman ya ce laifukan sun hada da na rubar da ciki da karin jini ba kan ka'ida ba. Gwamnati bata basu izinin su zubzr da ciki ba. Haka ma ba'a basu izini su kara jini ba. Ya ce wadannan mayan laifuka ne kuma duk asibitin da aka sameshi da laifukan idan an rufeshi ba za'a sake budeshi ba. Wato su asibitoci ashirin din da aka rufe wadanda suka aikata laifukan ba za'a sake budesu ba. Haka ma idan ma'aikatan asibiti basu da takardun kwarai ko kuma basu da tsafta ana rufesu.

Bugu da kari gwamnatin jihar tana sa idanu kan likitocin dake aiki da gwamnati amma kuma sun bude nasu asibitocin. Dr Usman ya ce likitan gwamnati na iya bude nashi asibitin to amma sai ya gama aikin gwamnati kafin ya je yin nashi. Idan aka lura cewa ya fi ba asibitinsa fifiko wurin yin aiki to zasu shiga takunsaka da gwamnati.

Mustapha Nasiru Batsari nada karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG