Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ba Ta Da Hurumin Karbar Kudin Da Ibori Ya Wawure - Falana


Abubakar Malami
Abubakar Malami

Fitaccen lauyan nan mai rajin kare hakkin bil’adama, Femi Falana, ya yi kira da a dawo da zunzurutun kudadden da tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori ya wawure ya kai kasar waje da suka kai fam milyan 4 da dubu 200 ruwa, cikin lalitar gwamnatin yankin Naija Delta.

Falana ya yi wannan kiran ne a yayin zantawa da gidan talabijan na Channels inda ya ce gwamnatin tarayyar kasar ba ta da hurumin karbar kudadden a bisa doka.

Malami
Malami

Falana ya kara da cewa, ya kamata a yaba da namijin kokarin da gwamnatin Najeriyar ta yi na bin kadin lamarin, ta hanyar hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arziki zagon kasa karkashin jagorancin ministan shari’a Abubakar Malami da tsohon shugaban hukumar Nuhu Ribadu, da hadin gwiwar ‘yan sandan Metropolitan na kasar Burtaniya.

Karin bayani akan: jihar Delta, James Ibori, Abubakar Malami, Nigeria, da Najeriya.

Duk da yabawa kokarin gwamnatin tarayya wajen aikin dawowa da kudadden, Falana ya ce, ya zama wajibi a maida kudadden jihar da aka wawure su.

Ministan shari’a na kasar Abubakar Malami, ya bayyana cewa, kudadden sun zarta fam milyan 100 kuma Burtaniya ta saki kashin farko da suka kai fam milyan 4 da dubu 200.

Abubakar Malami
Abubakar Malami

Daga karshe dai, Falana ya ce, kamata a biya diyya ga mutanen jihar Delta da lamarin ya shafa duk da cewa, a kasar burtaniyya a ka hukunta tsohon gwamnan jihar ta Delta kamar yadda sashin doka na 35 na majalisar dinkin duniya da aka kasashen Najeriya da Burtaniyya suka amince da ita.

Dokar da ta ayyana cewa, a baiwa mutanen da lamarin ya shafa duk kudadden da aka kwato sakamakon almundahana.

Falana dai ya bayyana matsayin na sa ne kwana 1 bayan da gwamnatin burtaniyya ta rattaba hannu a kan yarjejeniyar fahimta na maido wa Najeriya da kudaden da suka kai fam milyan 4 da dubu 200 da tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori, ya wawure.

Malami
Malami

Jakadiyar Burtaniyya a Najeriya, Catriona Laing, ce ta bayyana matsayin gwamnatin kasar ta Burtaniyya na dawo da kudadden da aka kwato daga ‘yan uwa da abokan tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori, a birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

XS
SM
MD
LG