Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Sace Masu Hakar Ma’adinai 100 Tare Da Kashe Wasu Mutane 10


Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle.
Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle.

Sarkin masarautar Anka na jihar Zamfara, Attahiru Ahmad, ya bayyana cewa, ‘yan bindiga dadi sun yi garkuwa da masu hakar ma’adinai sama da 100 da ke aiki tsakanin kananan hukumomin Anka da Marun a ranar 2 ga watan Maris da mu ke ciki.

Basarake Ahmad, dake zama shugaban majalisar sarakunan jihar Zamfara, ya bayyana hakan ne a birnin Gusau, fadar gwamnatin jihar a ranar talata a yayin da babban hafsan tsaron Najeriya, Lucky Irabor, ya jagoranci sauran manyan hafsoshin tsaron kasar a ziyarar aiki da suka kai jihar.

Basarake Ahmad, ya kara da cewa, lamarin ya auku ne a lokacin da hankulan gwamnatin da al’umman jihar ya karkata ga aikin kubutar da yaran makarantar gwamnatin Jangebe 279 da ‘yan bindiga suka yi awun gaba da su a ranar 26 ga watan Febrairun shekarar 2021 da mu ke ciki.

Hotunan yadda aka tarbi daliban makarantar Jangebe a fadar gwamnatin jihar Zamfara
Hotunan yadda aka tarbi daliban makarantar Jangebe a fadar gwamnatin jihar Zamfara

Kazalika, Sarki Ahmad, ya ce ‘yan bindigan sun kuma halaka wasu mutane 10 a lokacin da suka kutsa cikin wani filin hakar ma’adinai a cikin jihar.

Karin bayani akan: Zamfara, Bello Matawalle, AK-47, Nigeria, da Najeriya.

An dade ana kai ruwa rana game da ayyukan ‘yan bindiga dadi a jihar Zamfara da sauran jihohin arewa maso yamma inda suke far wa masu hakar ma’adinai don kwace kudadde da dukiyoyin su kamar yadda majiyoyin tsaro ke bayyana.

An jiyo basarake Ahmad na cewa, al’umman jihar Zamfara sun yi mamakin yadda gwamnatin tarayya ta ayyana dokar harmta zirga-zirgar jiragen sama sakamakon zargin kwararowar bindigogi a jihar duk da cewa ba bu alaka tsakanin ‘yan bindigan da masu hakar ma’adinai kuma ba ma filin tashi da saukar jiragen sama a jihar ta Zamfara ya na mai cewa, akwai jihohin da ke fama da matsalolin tsaro masu tarin yawa, kuma suna ganin cewa, idan gwamnatin Najeriya zata dauki irin wannan mataki kamata ta yi a irin wadannan jihohi masu fama da matsalolin tsaro.

Masu hakar ma’adin masu lasisi a jihar dai na taimakawa matuka wajen bunkasa tattalin arzikin jihar kuma suna taka muhimmiyar rawa a fannin rage radadin da ‘yan gudun hijira ke ji a jihar ta hanyar tallafi, in ji basarake Ahmad ya na mai mika bukatar gwamnati ta turo karin jami’an tsaro ruwa jihar ta Zamfara tare da yaba wa yunkurin gwamnatin jihar na yin sulhu da ‘yan bendiga dadi.

Daga karshe dai, Sarkin Anka, ya bukaci hukumomin tsaron kasar su hada gwiwa don tabbatar da cewa an samu nasara a yaki da matsalolin tsaro a jihar ta Zamfara.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG