Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa, Hafsat Ganduje da wasu mutane 6 zasu gurfana a gaban kotu a gobe Alhamis domin fuskantar tuhume-tuhumen dake da nasaba da cin hanci da rashawa da karkatarwa da kuma wawure kudaden da suka kai biliyoyin nairori.
Wata babbar kotun jihar Kano ce ta bada umarnin a ranar 5 ga watan Yunin shekarar da muke ciki, wanda ya baiwa gwamnatin Kano damar mika sammaci ga wadanda ake kara su 7 ta hanyoyin da bana hannu da hannu ba, inda daga bisani aka aiwatar da hakan ta hanyar wallafa sammacin a jaridun kasar nan guda 2, a ranar 6 ga watan Yunin daya gabata.
Wadanda ake karar sun hada da Dr. Abdullahi Ganduje (wanda ake kara na 1) da mai dakinsa Hafsat (wacce ake kara ta 2) da Abubakar Bawuro (wanda ake kara na 3) da Umar Abdullahi (wanda ake kara na 4) da Jibrilla Muhammad (wanda ake kara na 5) da masakar “Safari Textile LTD” (wacce ake kara ta 7) da kuma kamfanin “Lesage General Enterprises (wanda ake kara na 8).
Alkalin kotun, Mai Shari’a Amina Adamu, ce ta bada umarnin sakamakon bukatar da lauyan gwamnati, Zahraddeen Kofarmata, wanda ya wakilci babban lauyan masu kara, Ya’u Adamu, ya gabatar.
Ana sa ran a fara sauraron karar da misalin karfe 10 na safe a babbar kotun jihar Kano a gobe Alhamis.
Dandalin Mu Tattauna