Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Miyetti Allah Ta Yabawa Tinubu Da Ya Kirkiri Ma’aikatar Bunkasa Kiwon Dabbobi


Shugaban Miyetti Allah, Baba Usman-Ngelzarma
Shugaban Miyetti Allah, Baba Usman-Ngelzarma

Shugaban kungiyar ta MACBAN, Baba Usman-Ngelzarma, ne ya bayyana hakan a cikin wani shirin hantsi na tashar talabijin ta Channels mai taken “Sunrise Daily” na yau Laraba.

Daya daga cikin kungiyoyin makiyaya ta Najeriya, “Miyetti Allah Cattle Breeders Association Of Nigeria (MACBAN), ta yabawa Shugaba Bola Tinubu game da kirkirar Ma’aikatar Bunkasa Kiwon Dabbobi a kasar.

Shugaban kungiyar ta MACBAN, Baba Usman-Ngelzarma, ne ya bayyana hakan a cikin wani shirin hantsi na tashar talabijin ta Channels mai taken “Sunrise Daily” na yau Laraba.

Shugaban na MACBAN ya jinjinawa Shugaba Tinubu game da kirkirar ma’aikatar a lokacin da ya dace, sa’ilin da muke matukar bukatarta fiye da kowane lokaci.”

A cewarsa, “wannan shine abinda muka jima muna hakilon gani kuma gashi yau, mun same shi. Mun yi matukar murna da farin ciki. An sabunta fatanmu karkashin ajandar shugaban ta sabunta fatan ‘yan Najeriya.”

Shugaban kungiyar ta Miyetti Allah yace har yanzu Najeriya ba ta cin gajiyar kiwon dabbobi kamar yadda makwabtanta ke ci amma yanzu da wannan ma’aikata, kasar faso gardin tattalin arzikin dake fannin, tare da samun karin guraben aikin yi.”

Ya kuma bayyana fatan sabuwar ma’aikatar zata tabbatar samar da sauye-sauye a bangarorin “kiwon dabbobin da sarrafa albarkatunsu da safararsu da gudanar da fannin baya ga batun tsaro a harkar kiwon dabbobi a najeriya.

Jiya Talata, a babban dakin taro na fadar shugaban kasa dake Abuja, Tinubu ya bayyana cewar ana sa ran matakin ya kawo karshen yawan tashe-tashen hankula da ake samu a duk shekara tsakanin manoma da makiyaya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG