Mohammed Idris, Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa ne ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai na fadar Shugaban kasa, jim kadan bayan kammala taron kwamitin Shugaban kasa kan bada agajin gaggawa na abinci, wanda aka gudanar a fadar Shugaban kasa a Abuja.
Ya ce Shugaban kasar ya ba da umarnin cewa “za a samar da dukan abincin da ake bukata.”
Shugaba Bola Tinubu ya nuna za a iya shigo da abinci daga ketare don kara kayan masarufi idan an samu gibi a noman gida.
Gwamnatin tarayya ta kuma ja kunnen masu boye abinci, inda tayi kira ga jama’a su nuna kishin kasa a halin da ake ciki, ya kuma tabbatar da cewa, gwamnatin tarayya a shirye take ta zartar da hukunci kan musu boye abincin.
Matakin dai ya biyo bayan zaman tattaunawa da kwamitin ya yi, dangane da zanga-zangar da ‘yan Najeriya suka yi kan tsadar abinci da sauran kalubalen tattalin arziki.
Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC, da kuma kungiyar ‘yan kasuwa, TUC, sun baiwa gwamnatin tarayya sanarwar fara yajin aikin a fadin kasar dangane da tsadar rayuwa, wanda zai fara cikin kwanaki 14.
Kokensu ya samo asali ne daga gazawar gwamnati wajen aiwatar da yarjejeniyar mai kunshe da abubuwa 16 tsakanin kungiyoyin kwadago (NLC da TUC) da gwamnatin tarayya a ranar 2 ga Oktoba, 2023.
Dandalin Mu Tattauna