Jiya a Yaounde babban birnin ksar Kamaru Firayim Ministan kasar kuma shugaban gwamnati ya rantsar da wasu ministoci da suka cike gurbin wadanda aka kora.
Yayinda yake rantsar dasu Firayim Ministan ya yi fatan zasu yi aikinsu cikin gaskiya da adalci. Ya jaddada masu cewa gwamnatin kasar ba zata yadda da almundahana ba ko cin hanci da karbar rashawa. Yace duk wanda aka kama da irin wannan halin zai dandana kudarsa tare da fuskantar fushin gwamnati.
Wani tsohon dan siyasa kuma dan hamayya Sale Shaba yace nadin sabbin ministoci nada kyau da fatan zasu kula da kyau saboda su gyara aikinsu. Yace furucin Firayim Ministan ya yi daidai domin an dade ana cewa ministoci basa aikata ayyukansu daidai.
Yace shugaban kasa mai hakuri ne. Ya sha yin hakuri da ministocin da aka kora yana jiran su gyara halayensu amma basu yi ba. Saboda haka korarsu da cike gurbinsu da wasu daidai ne domin talakawa na wahala.. Sun yi marhaban da sabbin ministocin amma wadanda aka kora idan an samesu da yin ba daidai ba to hukumtasu ba zai zama laifi ba.
An gargadi kowane ma'aikacin gwamnati ya yi aiki bisa gaskiya tare da hada kai da sauran ma'aikata domin a samu cigaba. Gwamnati na fatan kowa zai rike amana domin na baya su yi koyi da dabi'u masu kyau..
Ga karin bayani.