Muryar Amurka ta zanta da Ardo Umaru Malam Zabbo hakimin garin Malam Zabbo, daya daga cikin garuruwan da Fulanin suka kafa a karkashin shirin gwamnatin kasa.
Ya nuna farin cikinsa da sabon shirin. Yace sun gode da ranar da gwamnati ta kebe domin yin bikin tunawa dasu. Yace ba zasu manta da ranar ba. Ya godewa gwamnati ya kuma kira ita gwamnatin ta kula dasu. Suna son a sansu su ma su zama mutane dake cikin jama'a.
Da dai an san Fulani da kaura daga wannan wuri zuwa can to ko menene zasu yi yanzu? Ardo yace yawan kauran da suke yi ya sa sun zama kaman mutanen dake baya a duniya. Saboda suma a dama dasu shi ya sa suka daina kaura. Yanzu sun soma zama wuri daya. Yanzu sun rabu da kaura.
Batun tura yaransu makarantar boko Ardo yace yanzu kam suna aniya. Sun daura damarar tura yaransu makaranta.Yace duk inda Fulani suke suna zama suna gina gidaje suna da tasu makarantar. Suna sa yara mata da maza makaranta.
Matsalar da suke fuskanta yanzu ita ce ta samun biyan malaman makaranta. Basu samun malaman makaranta na gwamnati. Su ne suke biyan malaman. Mai 'ya'ya da yawa kuma idan bashi da karfi dole ya tura wasu ya bar wasu.
Ardo Umaru kansila ne yana kuma jan hankulan Fulani 'yanuwansa akan alfanun zama wuri daya maimakon yin kaura. Shi yanzu yace ya soma jin dadi.Yana son su zauna su yi makaranta.
Suna rokon gwamnati ta taimakesu.
Ga rahoton Manmadu Danda.