Wannan canjin ya taba guraban ministoci 15 daga cikin 64 da kasar take dasu, tsoffin minstoci 6 ne aka canza wa wurin aiki.Kana 9 daga cikin su kuma aka sallame su.
Su dai wadannan taran ana zargin su ne da rashin iya aiki dama almundahana da kudaden gwamnati.
Wannan shine yasa shugaban kasar ta Jamhuriyar Kamaru Paul Biya yace dole ne ayi musu binciken kwa-kwaf.
An samu sababbin huska na ministoci su 9, ta bangaren sakatarorin gwamnati kuma shugaban kasan ya saka wasu sababbi 4, sai mai bashi shawara mutum guda.
Ga Muhammam Awal Garba da Karin bayani.