An fi samun jabun magungunan kashe kwari da takin noma.
Ana samunsu barkatai a kasuwanni aka farashe mai rahusa.
Ana hada magungunan ne ta hanyar da bata dace ba kuma wasu ma dake hadasu basu kware ba.
Manoman da basu san hawa ba balle sauka suna sayan kayan saboda araharsu suna anfani dasu a gonakansu lamarin da kuma yake jawo masu illa daga baya.
Ministan raya anfanin noma ya kirkiro da wani shirin fadakar da kawunan jama'a akan magungunan da gwamnati ta amince da su da magunguna na feshi da kuma irin ijinan da ake anfani dasu.
Ministan ya hada manoma da masu hada magungunan da suke da kyau domin su yiwa manoman cikakken bayani. Manufar ita ce a fada masu abubuwan da a da can manoman basu sani ba.
Gwamnati na son manoma dake zaman kansu su hada kai da ma'aikatan gwamnati domin a kawar da masu sayar da magungunan jabu a kasar. Idan sun san illolin dake tafe da sayan jabun magani zai taimakesu matuka domin lafiyar shuka kamar ta dan Adama take..
Ga rahoton Manmadu Danda.