Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Matawalle Ya Amince Da Daukan Sabbin Malaman Jami’a 412 A Zamfara


Gwamnan Zamfara Bello Matawalle (Facebook/Gwamnatin Zamfara)
Gwamnan Zamfara Bello Matawalle (Facebook/Gwamnatin Zamfara)

A wani mataki na farfado da kuma inganta bangaren ilimi a Jihar Zamfara, gwamna Bello Matawalle ya  amince da shawarwarin masu ruwa da tsaki na bangaren ilimi na daukan sabbin malamai 412.

ZAMFARA, NIGERIA - Za a dauki malaman ne a fannin koyarwa da wadanda ke aikin gudanarwa na dindindin da zasu yi aiki a jami’ar gwamnatin Jihar Zamfara.

Malamai suna jarabawa (Facebook/Gwamnatin Borno)
Malamai suna jarabawa (Facebook/Gwamnatin Borno)

Wannan matakin dai ya biyo bayan shawarar farko da hukumar gudanarwar jami'ar ta gabatarwa gwamnatin Jihar karkashin jagorancin gwamnan Jihar, Dakta Bello Matawalle.

Shugaban ma’aikata na gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad Kabiru Gayyari, ya tabbatar da amincewar gwamnan wanda zai fara aiki nan take.

A wani rahoton kwamitin dabaru da ci gaba karkashin jagorancin Farfesa Yusuf Muhammad Adamu Tsafe, tun da farko gwamna Matawalle ya umurci ma’aikatar ilimi a bangaren karatun gaba da sakandare da ta hada kai da hukumar gudanarwar jami’ar gwamnatin Jiha wato ZAMSUT don tabbatar da aiwatar da dukkan muhimman shawarwarin da za su saukaka daukar matakin ga jami'ar.

Bukin Ranar Malamai Ta Duniya A Dakin Taron Kungiyar Malamai Dake Jihar Adamawa
Bukin Ranar Malamai Ta Duniya A Dakin Taron Kungiyar Malamai Dake Jihar Adamawa

Dangane da aiwatar da wannan umarnin da shawarwarin rahoton da kwamitin Farfesa Yusuf ya bayar, mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Yahya Zakari Abdullahi ya gudanar da aikin daukar ma’aikata na koyarwa da na gudanarwar.

Ma’aikatar ilimi na gaba da sakandare mai zurfi ce ta kula da tsarin dauka aikin ta yadda ya yi daidai da sharudoddin hukumar kula da jami’o’i ta kasa wato NUC da kuma ka’idojin ma’aikatan Jihar Zamfara.

Haka kuma, daga cikin sabbin ma’aikata 412 da gwamnati ta amince a dauka, su 205 malaman koyarwa ne kuma an nada su a matsayin ma'aikatan ilimi a mukamai daban-daban da suka hada da masu matsayin farfesa, masu karatu, manyan malamai, malamai na I, malamai II, mataimakan malamai, da mataimakan da suka idda karatu.

Daliban Kaya a jihar Zamfara
Daliban Kaya a jihar Zamfara

An dai rarraba mukaman malaman koyarwa da na gudanarwar a duk bangarorin da ke cikin jami'a, waɗanda suka haɗa da sashen kimiyyar aikin jinya wato Nursing, kiwon lafiyar jama'a, sashin physiotherapy, sashin kula abinci masu gina jiki na ɗan adam, sashen kula da nazarin duniya da kasa wato Geology, reshen kimiyya wanda ya shafi yanayi da kwayoyin halitta da makamashi wato Physics da dai sauransu.

Sauran sun hada da sashen yanayi na Electronics, Biochemistry da Molecular Biology, Kimiyyar Kwamfuta, Biology, Chemistry, Mathematics, Statistics, Lissafi, Tattalin Arziki, Turanci, Tarihi da Nazarin Ƙasashen Duniya, Nazarin Musulunci, sashen Ilimin Yara, Ilimin Firamare, da aikin jarida.

Saura ma’aikata 207 da aka dauka a fannin da ba na koyarwa ba an dauke su ne a mukamai daban-daban da suka hada da mataimakan magatakarda, manyan mataimakan magatakarda, manyan jami’an zartarwa, mataimakan gudanarwa, manyan akawu, masana fasahar kere-kere, Manazarta tsare-tsare, manyan ma’aikatan kera-keran kimiyya da fasaha, jami’an cibiyar adana liattafai, Sakatarori, Ma’aikatan Kwamfuta, Ma’aikatan Lafiya, Masu Sana’a, Jami’an Kiwo, da Jami’an Fasaha, da sauransu.

Tuni dai gwamna Matawalle ya umarci shugaban ma’aikata da ya mika takardar amincewa ta hannun ma’aikatar ilimi ga jami’ar don a fitar da wasikun sanar da samun aiki ga duk wanda ya yi nasara.

Gwamna Matawalle ya kuma bukaci dukkan sabbin wadanda aka dauka aiki da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu domin ci gaban jami’ar da ma Jihar baki daya.

Kazalika, gwamnan ya kuma yi alkawarin ci gaba da baiwa sabuwar jami’ar da aka kafa dukkanin goyon bayan da ake bukata domin biyan bukatun da ake bukata na zama jami’a mai daraja ta duniya.

XS
SM
MD
LG