Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kashi 31% na malamai a jihar Borno kawai suke da kwarewar aiki- kwamitin bincike


Gwamna Zulum na jihar Borno (Facebook/Gwamnatin Borno)
Gwamna Zulum na jihar Borno (Facebook/Gwamnatin Borno)

Rahoton binciken da wani kwamiti da gwamnatin jihar Borno ta kafa domin nazarin ingancin harkokin ilimi a jihar ya nuna cewa, galibin malaman da ke koyarwa a jihar ba su da kwarewa.

A jiya Alhamis ne 17 ga watan Fubrairu 2022 Kwamishinan harkar ilmi na jihar Borno, Lawan Wakilbe ya gabatarwa gwamna da rahoton binciken.

Sakamakon binciken ya nuna malamai 17,229 da ake da su na nuna cewa, malamai 5,439 (31.6%) ne kawai suka dace su koyar, yayin da malamai 3, 815 ba su cancanci koyarwa ba. An gano cewa babu wani horo da wadannan malamai fiye da 3, 800 (22.1%) za su iya dauka. Akwai kuma wasu 2,389 (13.9%) da suke aiki ba tare da takardu ba.

Binciken ya kuma bayyana cewa, a yankin Abadam da ake da malamai 224, 14 daga ciki kawai suka cancanta su yi aikin koyarwa, 74 suna bukatar karin horo, 136 kuwa ba za su iya daukar horo ba.

Rahoton ya ce idan aka bi diddigi, haka abin yake a Kala-Balge inda malamai 21 suka ci wannan jarabawa, 133 su na neman horo, 118 ba su cancanta su yi aikin malanta ba. Yayinda aka fi samun malaman da ba su cancanta su rika koyar da yara ba a Maiduguri. Alkaluman na nuni da cewa, Askira-Uba, Chibok, Biu da Bama ne suka biyo bayansu.

Malamai 2, 281 da ake da su a jihar Borno su na aiki ne da takardar shaidar SSCE/GCE, ragowar 2, 389 da suka rage kuma su na aiki ba tare da su na da shaidar karatu ba.

A jawabinsa bayan karbar sakamakon binciken, gwamna Babagana Zulum ya yaba da aikin kwamitin, inda ya ce dole a gyara harkar ilmi a jihar. Zulum ya ce ba zai kori malaman da ba za su iya aikin koyarwa ba sai dai zai maida su zuwa wasu wuraren dabam su yi aiki kamar yadda aka bada shawara.

XS
SM
MD
LG