Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Bikin Anant, ‘Dan Shahararren Mai Kudin Asiya


Anant Ambani, mai shekaru 29, da budurwarsa da suka dade tare Radhika Merchant
Anant Ambani, mai shekaru 29, da budurwarsa da suka dade tare Radhika Merchant

Shahararrun ‘yan kasuwa na duniya da ‘yan siyasa sun fara hallara babban birnin kasar India a ranar Juma’a domin halartar daurin auren karamin dan Mukesh Ambani, wanda ya fi kowa arziki a Asiya.

Anant Ambani, mai shekaru 29, ya auri budurwarsa da ta dade suna tare Radhika Merchant, a wani abu da mutane da yawa suka kira gagarumin bikin aure na shekara.

Liyafar sa albarka ga ma’auratan
Liyafar sa albarka ga ma’auratan

Bikin na gudana ne a cibiyar taron Jio World Convention Centre mallakar Ambani da ke Mumbai da kuma gidan danginsu.

Biki ne da aka kwashe watanni ana shirye-shirye na bukukuwan aure da ke dauke da wakoki daga fitattun jarumai ciki har da Rihanna da Justin Bieber.

Baki da suka halarta lokacin bikin Anant Ambani
Baki da suka halarta lokacin bikin Anant Ambani

An dai fara bikin na kwana hudu ne da bikin daurin auren na Hindu a ranar Juma'a, sannan za a yi gagarumar liyafa a karshen mako.

Jerin baki da suka halarci bikin dai ya hada da tsohon Firaministan Burtaniya Tony Blair da Boris Johnson da Shugaban Kamfanin Saudi Aramco Amin H. Nasser da Adele da Lana Del Rey da Drake da David Beckham, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka bayyana.

Bikin ‘dan shahararran mai kudi a Asiya
Bikin ‘dan shahararran mai kudi a Asiya

Tashoshin labarai na Talabijin sun kuma nuna mashahuran mutane kamar Kim Kardashian da ƙwararren ɗan kokawa da ɗan wasan Hollywood John Cena sun isa wurin bikin.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG