Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ya bada belin tsohon Ministan Lantarki, Saleh Mamman, akan kudi Naira biliyan 10 da mutum 2 da za su tsaya masa suma akan makamancin wannan adadi kowannen su.
Saleh Mamman ya gurfana a gaban kotu ne a bisa tuhume-tuhume 12 dake da nasaba da hada baki domin halasta kudaden haram da mallaka tare da amfani da kudaden da aka samu ta haramtacciyar hanya.
Da yake zartar da hukunci akan bukatar bada belin wanda ake kara, Mai Shari’a Omotosho ya bayyana cewa wajibi ne wadanda zasu tsaya masa su kasance sun mallaki kadarori a Abuja da darajarsu ta kai akalla naira miliyan 750.
Haka kuma kotun ta kara da cewa wajibi wadanda zasu tsaya masan su mika sahihan takardun kadarorin gareta tare da shaidar biyan haraji ta shekaru 3.
Har ila yau kotun ta bukaci wanda ake karar ya gabatar mata da bayanan banki da takardun tafiye-tafiyensa.
A maimakon hakan, kotun ta bayyana cewar wanda ake karar na iya samar da takardar banki mai dauki da adadin kudin da ta yanke a matsayin jingina kuma idan ya yi hakan ba sai ya samarda masu tsaya masa ba.
Daga bisani kotun ta dage zamanta zuwa ranar 25 ga watan Satumba mai zuwa domin fara sauraron karar.
Hakan na zuwa ne bayan da a jiya Alhamis Mai Shari’a Omotosha, ya bada umarnin adana Saleh Mamman a gidan gyaran hali na Kuje har sai an kammala sauraron bukatar bada belinsa.
Dandalin Mu Tattauna