Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gungun Wakilai 'yan Jam'iyyar PDP a Majalisar Tarayyar Nigeria, sun Chanza Sheka sun Hada Karfinsu da 'Yan Adawa


Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan
Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan

'Yan Jam'iyyar PDP a Majalisar wakilai ta tarayyar Nigeria, sun bada sanarwar komawa jam'iyyar adawa ta APC.

Wakilai Talatin da bakwai a majalisar tarayyar Nigeria, sun bada sanarwar cewa sun fice daga jam'iyyar dake mulki kuma suka yi takara karkashinta sun koma jam'iyyar 'yan adawa, wanda hakan ke zaman wani sabon kalubalen siyasa da nuna yatsa ga shugaba Goodluck Jonathan.

A ran laraba ce, wakilan dake karkashin inuwar jam'iyyar PDP suka bada sanarwar cewa sun chanza sheka zuwa cikin jam'iyyar adawa ta (APC). daukan wannan matakin ya baiwa jam'iyyar Adawa ta APC ta zama mai rinjaye kadan ke nan a majalisar tarayya, wadda ta jima tana karkashin jagorancin jam'iyyar PDP kusan tun shekarar 1999. Sai dai duk da haka, jam'iyyar PDP zata ci gaba da rike matsayinta na shugabar masu rinjaye a Majalisar dattawan Nigeria.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG