Guguwar Irma mai dauke da ruwan sama, ta fara tunkudar gabar tekun jihar Florida, yayin da mutane kusan dubu 75, suka samu mafaka a wasu wurare da aka tanada domin tunkarar wannan bala’i.
An yi kiyasin, guguwar za ta sauka da sanyin safiyar yau Lahadi, inda za ta fara tsallaka wasu tsibirai kafin ta doshi yammacin gabar tekun jihar.
Ya zuwa wannan lokacin guguwar tana matakin karfi na uku ne, duk da cewa a baya, an yi fargabar za ta karfafa, yayin da za ta doshi arewaci, bayan da ta baro kasar Cuba a jiya Asabar.
Tampa, shi ne birnin da aka yi kiyasin guguwar za ta fi abkawa, duk da hasashen da aka yi a baya, wanda ya nuna cewa birnin Miami da ke gabashin gabar jihar ta Florida ne zai fi fuskantar guguwar.
Gwamnan Florida Rick Scott ya ce jihar ta shiga matakin dokar ta-baci, yana mai cewa “yanzu ne mataki na karshe da kowa zai dauki matsaya ta hakika,” yayin da yake ci gaba da yekuwar jama’a su fice daga yankunan da aka ayyana a matsayin masu cike da hadari.
Ya kuma ta nanata kiransa ga ma’aikatan kiwon lafiya da masu ayyukan ba da agajin gaggawa, da su dage su fito idan guguwar ta lafa domin taimakawa jama’a.
Facebook Forum