Cibiyar Dake Kula da Guguwa ta Kasa tace “Guguwar Irma ta watsu a yammacin wani yanki na Cuba da kuma tsakiyar Bahamas” bayan tabar ‘barna mara kyan gani a wani bangaren na Yankin Caribbean.
Irma dai na tafiya ne ta bangaren Arewa maso Yamma da sauri na Mil 14 cikin awa guda kuma tana dauke da Iska mai karfin gaske dake gudun kilomita 240 cikin awa guda, kuma zata cigaba da ragargazar Cuba da Bahamas har zuwa asabar. Ana kyautata zaton Irma zata doshi yankin Florida Keys da kuma Kudancin Florida a safiyar Lahadi.
Karfin Guguwar Irma dai ya ragu zuwa mataki na hudu daga na biyar a safiyar yau Jumma’a. Masu hasashe sunce ana zaton zata kasance cikin karfin ta a yayin da zata iso Florida.
Tuni dai wannan Guguwa mai suna Irma ta shiga cikin littafan tarihi. Kwararru sun kira ta Guguwar Atlantic mafi karfi da aka taba aunawa. An sami rahoton mutuwar mutane goma ya zuwa yanzu a Tsibirin Caribbean sakamakon Guguwar.
Facebook Forum