Yanzu haka jihohin Amurka 15 hade da babban birnin kasar Washington DC sun kai karar gwamnatin shugaba Donald Trump a kotu, suna kalubalantarta da niyyar tsaida wani shiri da a karkashinsa ake hana a maida dubban daruruwan matasan da aka zo da su Amurka tun suna kanana kasashensu na asali.
A cikin karar da suka shigar jiya a tarayya dake Brooklyn ta New York, lauyoyin jihohin sunce matakin da gwamnatin Trump ta dauka na soke wannan shirin da a takaice da turanci ake kiransa “DACA”, mataki ne da ya sabawa kundin tsarin mulki domin zai iya hana a kare matasan da abin ya shafa daga a ci zarafinsu a karkashin shara’a.
Babban Atone-janar na jihar New York, Eric Schneiderman ya bayyana shirin na Trump da cewa shiri ne na “rashin Imani, maras hangen nesa kuma na mungunta.”
Musamman ma atone-janar din ya zargi shugaba Trump da cewa yana auna ‘yan kasar Mexico da ‘yan jinsin Latino ne kawai.
Izuwa yanzu dai fadar White House bata maido da wani martini ga shigar da karar da aka yi mat aba.
Facebook Forum