Wani jami’in kungiyar kwallon kafa ta Granada a kasar Sifaniya ta ce ba za ta yi tafiya da dan wasanta Shon Weissman ba zuwa karawar da za ta yi da Osasuna a gasar La Liga.
Granada ta dauki wannan mataki ne a cewar jami’in wanda ya nemi a sakaya sunansa don ta kare lafiyar Weissman wanda dan asalin kasar Isra’ila ne.
Isra’ila da Hamas sun barke da fada a ranar 7 ga watan Oktoba bayan wani harin ba-zata da mayakan Hamas suka kai yankin Isra’ila.
Jami’in kungiyar ta Granada da ya tabbatar wa da Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press wannan al’amari ya ce Weissman ba zai je birnin Pamplona ba.
Kafafen yada labarai a Sifaniya sun ruwaito cewa hukumomi na nuna damuwa kan abin da magoya bayan Osasuna za su iya yi wa Weissman bayan zargin cewa sun fusata da wani sako da Weissman ya wllafa a shafinsa na zumunta kan fadan da ake yi a Gaza.
AP ya ruwaito cewa tuni Weissman ya goge sakon.
Dandalin Mu Tattauna