Wannan ne karon farko a tarihi da aka yi waje da kungiyoyin kasar Spain a irin wannan gagarumar gasar Turai a matakin farko, inda Barcelona da Atletico da Sevilla suka gaza yin gaba daga matakin farkon zuwa zagayen 16.
Hatta Real Madrid dake zama zakara a yanzu, da tuni ta tsallake zuwa mataki na gaba ta sha ci 3-1 a hannunb Leipzig a ranar Talata, karon farko da ta yi rashin nasara a dukkan gasa a bana.
Tawagar ta Carlo Ancelotti, wacce za ta karbi bakuncin Girona a ranar Lahadi, tana kan gaba a teburin La Liga da maki 31, a gaban Barcelona da maki uku, wadda ta yi rashin nasara a hannun babbar abokiyar hamayyarta da ci 3-1 a karawar El-Clasico makonni biyu da suka wuce.
Ana sa ran kocin din dan kasar Italiya zai fafata da Girona da ‘yan wasa da suka saba taka masa leda ne kamar Karim Benzema, Luka Modric da Federico Valverde wadanda ba su buga da Leipzig ba lokacin da Real ta yi kasa a gwiwa a fafatawarta da sabuwar kungiyar kasar Jamus da ke taka leda a matsayi na biyu.