Pique, wanda ya lashe lambobin yabo da yawa karkashin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, da kuma gasar cin kofin duniya ta 2010 tare da tawagar kasar, bai samu tagomashi a kakar wasa ta bana karkashin kocin Barcelona Xabi Hernandez ba.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ya tabbatar da cewa wasan La Liga da za su yi da Almeria ranar Asabar ne zai kasance wasan shi na karshe.
Dan wasan mai shekaru 35, ya kasance dan wasa ne da ke tawagar Barcelona masu buga wasa akai-akai bayan da ya koma daga Manchester United a shekarar 2008, amma a cikin ‘yan shekarun nan ya fara fama da rauni akai-akai. Duk da haka, Edgar Saiz na Eurosport na Spain ya ce sanarwar abin mamakin ce.
“Abin mamakin ne sosai domin babu wanda ya yi tsammanin hakan,” in ji shi. “Gaskiya ne saboda rawar da ya taka, ana tsammanin zai yi ritaya a karshen kakar wasa ta bana, amma yanzu abin ya zama da ban mamaki.”
Shigar ‘yan wasa irin Eric Garcia da Ronald Araujo ya tilasta masa yin kasa a jerin ‘yan wasa a sansanin horos da ‘yan wasa na Nou.