Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Amurka, NASA, ta wallafa bidiyon wata karamar duniya mai suna Ceres dake kewaya rana a tsakanin duniyar Jupiter da ta Mars.
Ceres tana cikin nau'in kananan duniyoyin da ake kira "Dwarf Planets" a turance, kuma ita ce mafi kusa da rana daga cikin danginta.
Wannan bidiyon da ya nuna hotuna garau na duniyar Ceres, wanda ba a taba ganin hoton da ya dauku kamarsa na duniyar ba, an dauke shine da kumbon nan mai suna Dawn wanda ya kewaya duniyar ya dauki hotonta baki daya daga nisan kilomita dubu 13 daga doronta, da kuma wasu hotunan na baya-bayan nan da aka dauka daga nisan kilomita dubu 5 kacal daga doron duniyar.
Ceres ita ce curin kasa mafi girma a wani yanki na wannan falakin ranar bil Adama inda akwai miliyoyin curin duwatsu dake kewaya rana. Ana kiran wurin Asteroid Belt a turance.
Duniyar Ceres tana da fadin kilomita 950, watau kimanin kashi 1 bisa 8 na girman wannan duniyar bil Adama. Ga hoton bidiyon nan a kasa...