A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na Mata na duniya da akeyi a kasar Canada, kasar Brazil ta Lallasa kasar Korea ta kudu da ci 2 da nema a wasan da suka yi jiya a birnin Montrael.
Marta, ‘yar kasar Brazil, wace ta samu bugun da kai sai mai tsaron gida, a minti na 53, ciki wasan ta yi nasarar jefa kwallon a ragar Korea ta kudu wanda ya bata damar shigewa gaba ta kasance wace tafi cin kwallaye a tarihin gasar.
Marta, ‘yar shekaru 37, da haihuwa dai sau biyar take zama ‘yar kwallon da tafi kowa bajinta da kyau a wasab kwallo.
A wani wasan kuma da aka buga tsakanin kasashen Spain da Costa Rica, an tashi wasan kunnen doki 1 da 1, koda yake kasar Spain ta kaiwa Costa Rica , hare-hare amma mai tsaron gidan Costa Rica Dinnia Diaz, ta turje.
A ranar asabar Brazil zata kara da kasar Spain inda ita kuwa Costa Rica hadu da Korea ta kudu.