Hukumomi sun ce gobarar ta tashi da asubahin jiya lahadi a wannan gidan rawa da ake kira Kiss. Wadanda suka kubuta da rayukansu, sun ce wani daga cikin makida dake wasa a lokacin, shi ne ya kunna wani abin wasan wuta mai kama da Knockout ya cilla shi sama a dakin da suke wasa.
Da yawa daga cikin wadanda suka mutu, sun suke ne, ko kuma dai an tattaka su a lokacin da mutane ke kokawar fita daga cikin wannan gidan rawa.
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, yace yana jimamin wannan bala’i, musamman ma ganin cewa matasa da dalibai masu yawa haka sun mutu. Ya aike da sakonsa na ta’aziyya ga iyalan mamatan.
Shugabar kasar Brazil, Dilma Roussef, ta tsinke ziyarar da take yi a kasar Chile ta koma gida a jiya lahadi a bayan wannan gobara.
Santa Maria birni ne dake da babbar jami’a da kuma mutane kimanin dubu 250. Birnin yana kuryar kudancin Brazil a kusa da inda ta yi iyaka da kasashen Argentina da Uruguay.