Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Girgizar Kasa Ta Hallaka Mutane Sama Da 95 A China Da Tibet


Girgizar Kasa A CHINA/TIBET
Girgizar Kasa A CHINA/TIBET

Wata girgizar kasa mai karfin gaske ta girgiza yankin yammacin China mai yawan tsaunuka da wasu sassa na kasar Nepal a yau Talata, inda ta lallata daruruwan gidaje tare da cika tituna da baraguzan duwatsu da kuma hallaka akalla mutane 95 a yankin Tibet.

Haka kuma mutane da dama sun makale sakamakon gomman kananan girgizar kasar da ake ci gaba da samu a yankuna masu nisa.

Masu aikin ceto na hawa tarin fasassun bulo, yayin da wasu ke amfani da tsani a kauyukan da suka yi matukar lalacewa a kokarinsu na neman masu sauran numfashi. Faifan bidiyon da ma’aikatar agajin gaggawa ta China ta wallafa ya nuna yadda ma’aikata da ke dauke da wasu mutane 2 a kan gadon daukar marasa lafiya ke bi ta cikin baraguzan gidajen da suka rushe.

Akalla mutane 130 ne suka jikkata a yankin da girgizar kasar tafi yin ta’adi na lardin Tibet da ke bangaren China na kan iyaka, kamar yadda tashar talabijin din kasar China (CCTV) ta ba da rahoto, ta hanyar ruwaito mataimakin magajin garin birnin Shigatze.

Fiye da gidaje 1000 ne suka rushe a yankin saharar mai karancin jama’a, kamar yadda CCTV ta ruwaito. a bidiyon da kafar yada labaran ta wallafa, an ga yadda baraguzan gini suka cika tituna tare da latse motoci.

Al’ummar da ke zaune a yankin arewa maso gabashin Nepal sun ji motsawar girgizar kasar, sai dai ba’a kai ga samun rahotannin farko game da jikkata ko barna ba, a cewar cibiyar agajin gaggawa ta kasar.

Yankin Mount Everest (tsauni mafi tsawo a duniya), dake da nisan kilomita 75 daga inda girgizar kasar ta afku, ya kasance babu mutane saboda tsananin hunturu yayin su kansu mazauna yankin ke yin kaura zuwa yankunan kudanci domin gujewa sanyi.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG