Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Girgizar Kasa Ta Rusa Harkokin Yawon Bude Ido A Maroko


A view shows a helicopter flying over the devastated village of Adassil
A view shows a helicopter flying over the devastated village of Adassil

Ziyarar masu yawon bude ido zuwa tsaunukan Maghreb a baya ta kasance wata kafar samun kudaden shiga da ayyukan yi a yankin da ke fama da fatara.

Makonnin baya, kafin aukuwar ibtila’in girgizar kasar da ta girgiza Morocco, Abdessamad Elgzouli yakan jagoranci mutane masu zuwa kasar yawon bude ido, inda yake jagorantar su zuwa tsaunukan kasar dake yankin al'ummomin Maghreb kuma matsugunin kabilar Berber ko kuma Amazigh.

Yanzu sabuwar sana'ar Elgzouli ita ce taimakawa wajen kafa rumfuna a sansanoni a Amizmiz, inda daruruwan mutanen da suka rasa muhallansu a sakamakon girgizar kasar da ta auku cikin wannan watan su ke.

Elgzouli wanda yake kewaye cikin gidan shi wanda ya lalace duk da cewa bai rushe ba, ya ce, abin da ya wuce ya zama tarihi”.

Girgizar kasar mai karfin 6.8 a ma'auni ta kashe akalla mutane 3,000, ta kuma shafe gidaje a kauyukan da ke tsaunukan, kana ta lalata makarantu, asibitoci da gidaje a gundumomi 5 da lamarin ya fi shafa. Cikin ‘yan dakikai ta shafe tushen tattalin arzikin kasar na yawon bude ido wanda al’ummomin na Moropcco masu fama da talauci da karancin ci gaba suke alfahari da shi wajen samun kudaden shiga.

Yanzu yankin yana fuskantar matsalar sake farfado da gine-ginen da suka rushe a daidai sa’adda ake tunkarar yanayi mai tsanani na hunturu wanda zai sa aikin farfadowar ya yi matukar wuya sannan kuma ya dada ta’azar matsin rayuwa ga dubban ‘yan Marocco da ke rayuwa a cikin rumfunan da aka kafa a can tudun tsaunnukan.

Yayin da gwamnatin kasar ta yi alkawarin zuba tsabar kudi dala biliyan $11.7 da zummar taimakawa mutanen da girgizar kasar ta shafa su miliyan 4 sake farfado da rayuwarsu, kwararru sun ce matsalar kai dauki ta habbaka fiye da haka yadda ake tsammani. Tun farkon watan nan dai, wani binciken Amurka kan yanayi ya kiyasta ibtila’in cewa zai dada tsananta tabarbarewar arzikin kasa, kana ta yiwu ta lakume wa kasar kaso %8 daga kudaden shigan Morocco.

Baya ga haka kuma, ibtila’in ya dau wani salon siyasa yayin da gwamnatin kasar ta ki amincewa da karbar taimakon jinkai daga kasashe kamar makwabciyarta kuma abokiyar hammayarta, Algeria, da kuma iyayen mulkin mallakarta Faransa, kana, ta amince da taimakon wasu tsirarun kasashe kawai. Masu suka sun ce hukumomi sun yi jan kafa wajen daukar mataki.

Sarkin Morocco Muhammad na VI yana birnin Paris a lokacin da girgizar kasar ta auku. Kwanaki bayan nan kuma ya ziyarcinasibitoci dake biranen Marakesh da ibtila’in ya lalata.

Hukumomi sun kalubalanci sukar da ake musu sannan ‘yan Morocco sun bayyana martanin sakin da hukumomin kasar da girman kai. Kana sun nuna irin kayakin da aka taimaka musu da su kamar sutura, barguna, abinci da magunguna daga kasashe a fadin duniya.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG