Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GHANA: Gwamnatin Amurka Ta Gana Da Sarakuna Game Da Hakar Ma'adinai Ta Barauniyar Hanya


TAWWAGAR JAKADIYAN AMURKA TAREDA SARKIN ASANTI
TAWWAGAR JAKADIYAN AMURKA TAREDA SARKIN ASANTI

Gwamantin Amurka ta yi kira ga gwamnatin Ghana da ta cigaba da karfafa matakan da suka dace domin shawo kan matsalan hakar ma'adinai da ke cigaba da yin barazana ga tattalin arzikin kasar.

Jakadiyar Amurka a Ghana Virginia E.Palmer ce ta bayyana haka yayin da ta kai ziyara a masarautar Ashanti, daya daga cikin jihohin da hakar ma'adinai ta barauniyar hanya ya yi wa illa sosai.

A jawabinta, Jakadiyar ta bayyana cewa, "ko shakka babu hakar ma'adinai na gurbata muhallinku musamman ruwan sha , ya na tasiri akan cocoa dinku da anfanin gonakin ku. Wannan duk zai yi mummunan tasiri akan tattalin arzikin ku muddin ba'a dau matakai ba".

Masu hakar ma'adinai
Masu hakar ma'adinai

Jakadiyar Amurka ta kara da cewa, wata tawagar sashen kula da albarkatun kasa a Majalisar dattawan Amurka ta isa Ghana ta kuma tattaunawa da sarakunan gargajiya da mai alfarma Sarkin Asanti game da hakar ma'adinai ta barauniyar hanya.

TAWWAGAR JAKADIYAN AMURKA TAREDA SARKIN ASANTI
TAWWAGAR JAKADIYAN AMURKA TAREDA SARKIN ASANTI

A jawabinsa, mai alfarma Nana Otumfuo Osei Tutu Sarkin karkaran aladan Asanti , ya dora alhakin wannan matsala bisa wasu jami'an gwamnati musamman shugabannin gundumomi inda ya ce "gwamnati ta dau matakai ciki har da tura dakarun soja da 'yan sanda domin hana hakar ma'adinai amma har ila yau ba'a iya magance ta ba. Duk da cewa ana fama da matsalar rashin sana'a a kasar kamata yayi a dau matakin shawo kan wannan matsalar."

Daya daga cikin masu ruwa da tsaki bisa harkar hakar ma'adinai a kasar Ghana wato shugaban kungiyar hadin guiwar masu hakar ma'adinai a kananan filaye a jahar gabashin kasar Ghana, Muhammad Amao ya bayyana cewa, shugaban kasa na kokari, amma wasu jami'ansa ke yi ma wannan mataki zagon kasa.

Sai dai shugaban kungiyar masu hakar ma'adinai na bukatar a baiwa 'yan jarida tare da masu lasisin hakar ma'adinai damar shiga cikin masu yaki da wannan matsala.

Gwamati dai tace matakan da take dauka na tasiri musamman wajen tsaftace ruwan sha da sauransu.

Bincike na nuni da cewa, hakar ma'adinai ta barauniyar na bada tasiri wajen gurbata muhalli abinda ke barzana ga ruwan sha tare da tattalin arzkin kasar Ghana saboda sinadaran da ake anfani da su na gurbata cocoa din da kasar ke dogaro da shi wajen samun kudaden shiga.

Saurari rahoton Hamza Adam cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG