Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Da Wasu Kasashen Afirka 7 Za Su Kulla Yarjejeniyar Cinikayya Ta Shekaru Hudu


Shugaban Ghana Nana Akufo
Shugaban Ghana Nana Akufo

Kasar Ghana da wasu kasashe bakwai a karon farko sun amince da su fara gudanar da cinikayya tsakaninsu shekaru hudu bayan kulla yarjejeniyar gudanar da cinikayya tsakanin kasashen Afirka ba tare da shinge ba da ake kira AFCTA a takaice.

ACCRA, GHANA - Masana na nuni da cewa kasancewar kasuwanci a karkashin AFCFTA zai bunkasa kasuwanci a nahiyar, zai kuma sa farashin kayayyaki ya sauka, sannan kuma za a samu karuwar aikin yi ga jama’a.

Kasashen da za su fara gudanar da kasuwanci tsakaninsu, a karkashin yarjejeniyar cinikayya tsakanin kasashe da babu shinge a tsakani, ko AFCTA a takaice, sun hada da Ghana, Kamaru, Masar, Kenya, Mauritius, Rwanda, Tanzaniya da Tunisiya.

Hakan zai kara habbaka yawan fita da kayayyaki zuwa kasashen waje ta hanyar kamfanoni fidda kaya (ETC), sannan kuma a cin ma burin inganta masana’antu da za su taimaka wajen karawa nahiyar dogaro da kanta.

Mataimakin ministan cinikayya da masana’antu, Herbert Krapa ne ya bayyana hakan, da yake jawabi wajen taron karawa juna sani da ma’aikatarsa da hadin gwiwar bankin Afrexim suka shirya.

An shirya taron ne domin kara wayar da kan jama'a kan rawar da wadannan kamfanoni za su taka wajen ci gaban kasuwanci tsakanin kasashen Afirka, a karkashin yarjejeniyar ta AfCFTA.

Masanin tattalin arziki Hamza Adam Attijjany ya yi wa Muryar Amurka karin bayani cewa, yarjejeniyar za ta baiwa duk mambobin kasashen samun damar gudanar da kasuwanci a saukake.

Ya kara da cewa, bankin duniya ya nuna cewa idan an tabbatar da wannan yarjejeniya, za a bunkasa kasuwancin da Afirka za ta samu sama da dalar Amurka biliyan 160.

Masanan sun nuna cewa, harkokin kasuwancin idan aka gudanar da su cikin yanayi mai ‘yanci da tsaro, zai taimaka wajen rage talauci a mambobin kasashen kungiyar tare da samar da ci gaba mai dorewa.

Saurari rahoto cikin sauti daga Idris Abdullah:

Ghana Da Wasu Kasashen Afirka 7 Za Su Kulla Yarjejeniyar Cinakayya Na Shekaru Hudu.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

XS
SM
MD
LG